價格:免費
更新日期:2018-11-25
檔案大小:3.3M
目前版本:7.1
版本需求:Android 4.1 以上版本
官方網站:mailto:lassnaija@gmail.com
Abdullahi (RA) yace: Na tambayi Manzon Allah (SAW) cewa wane aikine Allah mai girma da daukaka yafi so sai yace: "Sallah akan lokacinta, sai nace sannan me? Sai yace: Bin Iyaye, sai nace sannan me? Sai yace: Sannan Jihadi don daukaka kalmar Allah. Sannan yace ya fada mun wainnan abubuwan kuma da naso ya karamun da ya karamin".
Abdullahi bin Umar (RA) yace: Yardan Allah yana cikin yardan iyaye, kuma fushin Allah yana cikin fushin iyaye. Wato wanda iyayensa suka yarda dashi to Allah zai yarda shi, haka ma idan iyayensa suna fushi dashi to Allah ma yana fushi dashi. A wani hadisin kuma
Abdullahi dan Abbas yace: Lallai ni ban san wani aiki wanda yafi kusanci zuwa ga Allah ba fiye da biyayya
ga Mahaifiya. [Duka hadisan suna cikin Al-Adabul Mufrad].
Allah kasa mu kasance masu farantama Iyayen mu